Rayuwa! Na Ibrahim Malumfashi

‘Salamu alaikum ko mutan gidan na ciki?’ Sallama ce daga waje.

‘Wa’alaikumus salam,’ yaro ne dan shekara 8 ya amsa mata.
Ta shigo cikin falon, ta yi tsaye da ta ga yaro ba ko riga yana kallon ta.

‘A’aaaha, ba kowa ne a cikin gidan, sai kai?’

‘Akwai kowa mana, ko ni ba kowa ba ne halan?’ Ya fada cikin yarinta.

‘Yi hakuri, ni ba baka na ce ka fada mini ba, daga tambaya!

‘Ai, akwai magana fara ne da kike batun baka? Abar dai zancen, duk sun fita, sun bar ni tsaron gida ne.’

‘Don Allah rufe man baki da yawan surutu, ta yaya kamarka zai tsare gida in ba hauka ba.’

‘Hauka? Ta yaya yaro kamana zai yi hauka, cewa nake yi sai manya ko ma’aikatan gwamnati ke yin hauka?’

Cikin mamaki ta ce da shi, ‘yaya kake ce da ma’akaitan gwamnati mahaukata?’

‘Haka na ji Baba na fada. Yana cewa ai mai aikin gwamnati shi ne mahaukaci yau a Nijeriya. Domin kuwa ba yadda za a yi idan ba hauka ba, mutum ya amshi albashin dubu talatin a wata, alhali shi yana bukatar dubu sittin ya ciyar da iyalinsa, ya yi mirsisi ya ce Allah ya kyauta,’ in ji Baba.

‘Ban gane ba, me Babanka ke nufi?’

‘Bari na yi maki Gwari-Gwari. Cewa yake yi hauka ne ka amshi albashin da ka san ba zai ci da iyalinka ba, a kuma zauna lafiya!’

‘Ta yaya mutum zai zama mai hankali idan da kai ne za ka yi bayanin da kyau,’ ta fada, ta kuma nemi wuri ta rashe.

‘Ai da in zama mahaukaci, gara in zama barawo!’ Ya ce da ita.

‘Haba kai ko, ta yaya za ka ce haka, barawo ai ba mutum ba ne.’

‘Shi ko mahaukaci fa, mutum ne? Ya tambaye ta.

‘Mutum ne mana, me kake nufi?’

‘Wallahi ni dai ban amsar abin da na san bai ciyar da iyalina domin in bauta wa gwamnati.’

‘Kai kuwa dana ai ba bauta ba ce, ba ka ganin cewa abin da ya dace a biya ka ke nan?’

‘Rabin hakkina a wata shi ne biya na? To ko ke ma kin soma irin nasu haukan ne?’

‘Ashe ba ka da kunya, ni kake ce wa mahaukaciya?’ Ta fada cikin kakkausar murya.

‘Allah ya huci zuciyarki, ba haka nake nufi ba. Amma don Allah ki fada mani gaskiya ke ma ma’aikaciyar gwamnati ce ko?’

‘Ehhh, ita ce, sai me?’ Ta fada a fusace.

‘A’a, ba komi’, ya fada cikin gunaguni.

‘Don Allah ka bayyana mini man, ba zan sake yin fushi da kai ba.’

‘To shi ke nan. Na san dai kin zo wurin mama ne ki roki sauran garin kwaki, to mu ma Baba ya jefa tiyar garin da ta rage cikin wata bakar leda, ya sa kirtani ya daure, ya dauki bakar ledar ya sa cikin wani kwanon sha, ya rufe, ya sa bisa silin din dakinsa ya boye!’

‘Saboda me?’ Ta ce da shi cikin mamaki.

‘Ai haka Baba yake yi duk tsakiyar wata, yana cewa ba a kara shan gari sai wata ya kusa karewa’.

‘Haba sai ka ce mahaukaci?’

‘Mahaukaci!’ Ya ce da ita.

‘Me ka ce?’

‘Na ce mahaukaci!’

‘Baban naka kake ce da shi mahaukaci?’

‘Yo ba ke kika ce in ce ba!’

‘To mu manta da wannan batun, ni ba garin kwaki na zo bida ba, dama ina son ku ‘yan mani ruwa ne, ba mu da ko tarfi a gidan, tun jiya da dare.’

‘Ai abin da nake gaya maki ke nan tun dazu. Ba kowa gidan, yayyena sun tafi bakin kasuwa inda famfon ya fashe, su gani ko za su kwakulo mana jarka guda, tun dazu ba su dawo ba.’

‘Ku ma naku famfon ya lalace ne?’ Ta ce da shi.

‘Ko alama, Mama cewa take a kullum, famfon namu gara babu da shi, domin kuwa rabon da ruwa ya digo daga jikin fanfom tun kafin a yi yayen ‘Yar lele, yau kusan wata shida ke nan.’

‘Ita Babar taku ina ta tafi?’

‘Ta leka wajen masu nikan masara ne ta ga me ya faru. Domin tun da safe ta aiki wana Kabir kai nika har yanzu ba su dawo ba?’

‘Ko ka san abin da ya hana Kabir dawowa da nikan?’

‘Na sani mana. Na gaya wa Mama kada ma ta damu kan ta, ba zai sami nikan ba sai da magariba, ta ki saurare na, ni kuma na kyale ta.’

‘Amma kai ko, ai dole ta bi shi saboda a sami garin da za a yi muku tuwon dare ko.’

‘Lallai haka ne. Amma ai abin da ba ta sani ba shi ne NEPA ba za ta kawo wuta ba sai da kusan magariba, a lokacin kuma Mushirikat ta tafi coci, ba kuma za su daina wake-waken da raye – rayen ba sai wajen takwas na dare. To ina amfanin bin yaya da ta yi?’

‘Ka sani ko tana son su kai nikan wajen injin ruwa ne!’

‘Uhum, ai injin ruwa daya ne kurum a unguwar. Kuma tun jiya na ji Iya Tawakaltu tana ce da Tawa, ta gaya wa mahaifinsu in ya dawo daga gareji ta tafi dauko injin din da ta kai gyara can kara, ba kuma za ta dawo ba sai gobe da safe.’

‘Kai ko wai yaya aka yi ka yi wayo haka?’

‘Ba wayo ba ne, rayuwa ce!’

‘Ban gane ba, wata makaranta ce kake zuwa ta rayuwa?’

Ya yi murmushi, ‘ai ko makarantar ma ban shiga ba!’

‘Me ya hana?’

‘Baba ya hana!’

‘Don Allah ka daina yi wa iyayenka karya, me zai hana su sa ka makaranta kai kuwa?’

‘Da wane kudin za su sa ni? Imam, babban wana na jami’a. Maijidda, mai bi masa na kwaleji. Isa da ke biye da ita, na firamare. A kowane zangon karatu Baba na bukatar sama da Naira dubu 90 ya biya musu kudin makaranta. Saboda haka ya ce ni in dan huta kafin wani lokaci. Shekara biyu ke nan ina hutawa.’

‘Haba yaro ya za a yi a kasa biya maka kudin makaranta saboda ‘yan uwanka na karatu?’

‘Hala dai ba ki yi makaranta ba ne?’

‘Me ya sa ka ce haka?’

‘Idan aka tara dubu 30 sau uku, nawa ke nan?’

‘Dubu 90!’ Ta ce da shi.

‘A kowane zangon karatu wata nawa ne, in ce uku?’ Bai jira ta amsa ba, ya ci gaba, ‘kin manta cewa albashin Baba dubu 30 ne kowane wata?’

‘To shi Baban naka bai iya yin komi ya samu kudin da zai cikasa ya sa ka makaranta?’

‘Yana iyawa!’

‘To me ya hana shi?’

‘Ban sani ba!’

‘Haba, yaro mai wayo kamarka zai ce bai sani? Don Allah gaya man hanyar da zai bi ya taimake ku.’

‘Hanya daya ce,’ ya fada da ajiyar zuciya.

‘Wace ce?’

‘Ya yi sata.’

Ta yi zambur ta mike tsaye. ‘Sata, haba dana, sata fa ka ce!’

Yana mamaki, ya ce da ita, ‘to laifi ne yin satar?’

‘Laifi ne mana!’

‘In laifi ne shi ne na yi ta gani a talbijin an nuno buhunan Gana-Mus-Go a majalisar Dattijai da ta Wakilai ana cewa daga ofishin Shugaban kasa ne, wai an aiko musu da cin hanci?’

Ta yi shiru.

‘Me ya same ki, na ji kin yi shiru?’

Ba ta amsa ba!

‘Kukan me kike, cinnaka ne ya cije ki, na ga kina zubar da hawaye?’

Ta sa hannu ta share hawaye da habar zanenta, ta ce ‘ba komi, kana ba ni tausayi ne kurum.’

‘In don ni ne kada ma ki damu kan ki, ba abin da zai same ni, domin Babana ya ce mu yara ba abin da zai same mu daga mahaukaciyar gwamnatin kasar nan.’

‘Wai wa ke koya maka irin wadannan miyagun kalamai ne haka?’

‘Babana!’

‘Shi ke koya maka zagi da bakaken maganganu irin wadannan?’

‘Ehh mana.Na ce maki ni ba na ko zuwa makaranta balle ki ce can na koyo. Rayuwa ce kurum! Idan ma kika ji yadda Baba ke bayani, ai ni ba komi nake cewa ba. Jiya na ji yana cewa ai shi bai ki duniyar ta watse ba. Yana cewa in ma an ga dama a yi tashin kiyama, yau ko gobe. Haka kuma na ji yana ta fadar bai taba ganin shegun shugabanni irin namu ba. Yana karawa da cewa bai taba ganin mugaye, macuta, mamugunta, azzalumai ba irin masu kudinmu. Da na ce da shi baba ta yaya kake neman a yi tashin kiyama a halin yanzu, me ya yi zafi….’

Nan take ta katse masa hanzari ta ce da shi, ‘kai amma ana cikin matsalaloli a kasar nan.’

‘A’a, ba a cikin matsaloli, mu tamu matsala daya ce kurum!’Ya ce da ita!

‘Wace ce?’

‘Yunwa!’

‘Shi ke nan?’

‘To kila talauci!’

‘Talauci?’ Ta tambaye shi.

‘Rashin boza mana, ko ba ki san wannan ba? Fatara. Rashin naira!

Ni ban san wannan ba!’

‘Karya kike yi wallahi?’

‘Kai dan abin uwar nan…. ni kake karyatawa!’

‘Ni ban karyata ki ba. Ba kuma ni na fada ba, Baba ne ya ce duk wanda ya ce bai san talauci a kasar nan ba, to mahaukaci ne ko kuma makaryaci?’

‘Me ya sa Babanka ke bayyana maka wadannan abubuwa marasa dadin ji da kuma ban takaici?’

‘Cewa yake saboda idan na girma ba zan hadu da matsaloli a rayuwa ba.’

‘Me zai faru gare ka in ka girma? Me yake hange?’

‘Matsaloli!’

‘To ai yana nan raye zai iya taimakonka ko!

‘Ya ce kafin ya mutu zan san hanyoyin magance matsalolin rayuwa.’

‘Me zai sa ya mutu?’

‘Matsalolin rayuwa mana!’ Fashi da makami. Sace-sacen mutane. Karuwanci da zina da madigo. Kashe mutane da yankar kai da kuma hadama da babakere. Kai ga su nan bilahaddin….In ji Baba!
Ta yi ajiyar zuciya, sa’annan ya ji tana cewa,‘Allah ya isa, Allah ya tsine. Allah wadarai. Allah ka fatattaka wadannan musu bata mana rayuwa da ta yara irin wannan. Allah ka sa su shiga cikin kunci da muke ciki, ko ma nasu ya fi haka. Allah, idan masu gyaruwa ne ka gyara su, idan ko ba masu gyaruwa ba ne, Allah ka kashe su, ka kashe su na ce!’

‘Me ya sa kike irin wadannan miyagun maganganu ke ma, ko kina zuwa makarantarmu ne?’ Ya ce da ita.

‘Wace?’

‘Ta rayuwa!’

Ba ta amsa masa ba.

‘Shegu!’ Ta fada cikin kakkausar murya.

Ya fashe dariya, ‘ke ma kin soma magana irin ta Baba.’

‘Allah ya isa! Ai ni wallahi da zan ga inda aka ajiye kahon nan, wallahi da na dauko shi na hura shi yanzu-yanzu, kowa ya huta. Takadarun azzalumai kawai!’

Ta mike za ta wuce, ta ce da shi, ‘ka gaya wa Babarka cewa na leko, idan kuma ta rage tuwon jiya ta aiko ka da shi, domin yaran gidana tun safe rabon su da su jefa wani abu a uwar hanjinsu.

‘To za ta ji.’ Ta fice. Shi kuma ya yi zaune zugudum, yana magana a hankali, ‘ka ji maras hankali ko. To ta aiko maki da sauran tuwo, mu kuma mu ci me?’

DON’T MISS OUT!
Subscribe To Newsletter
Be the first to get latest updates and exclusive content straight to your email inbox.
Stay Updated
Give it a try, you can unsubscribe anytime.

2 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here